Kakakin rundunar sojin kasar Yemen Birgediya Janar Yahya Sari’e a jiya Alhamis ya bayyana a cikin wata sanarwa da aka watsa ta gidan talabijin din kasar cewa: Farmakin farko da sojojin Yemen suka kai kan wani jirgin ruwa ne mai suna (Verbena) a cikin tekun Arabiya, kuma sun harba makamin ne kai tsaye kan jirgin, lamarin da ya sa ya kama da wuta.
Ya kara da cewa: Ayyukan na biyu da na uku sun kai hare-hare ne kan jiragen ruwa na “Seaguardian” da “Athina” a cikin tekun Bahar Maliya, kuma suna ci gaba da kai hare-hare kai tsaye jiragen makiya da suke tallafawa ayyukan wuce gona da irin yahudawan sahayoniyya.
Janar Yahya Sari’ie ya tabbatar da cewa: Sun gudanar da ayyukan uku ne da makamai masu linzami na ruwa da jirage marasa matuka ciki, kuma sun samu nasarar cimma burinsu.