Isra’ila Na Ci Gaba Da Kai Hare-hare A Zirin Gaza A Daidai Lokacin Da Ake Dakon Sasantawa

Isra’ila, na ci gaba da kai hare-hare a Gaza, a daidai lokacin da ake dakon fatan samun sasantawa. Fadan dai ya fi karkata ne a

Isra’ila, na ci gaba da kai hare-hare a Gaza, a daidai lokacin da ake dakon fatan samun sasantawa.

Fadan dai ya fi karkata ne a yankin Rafah da ke kudancin Falasdinu, inda a farkon watan Mayu sojojin Isra’ila suka kaddamar da hare-hare ta kasa.

Bayanai sun ce ko a jiya an yi musayar wuta sosai tsakanin sojojin Isra’ila da mayakan ‘yan Hamas.

Sojojin Isra’ila sun kai hare-hare da manyan bindigogi da kuma jiragen sama a yankuna da dama ciki har da Rafah da ke kudancin zirin Gaza.

Bangaren sojan Hamas ya ce an gwabza fada ne a kan tituna a yammacin Rafah inda shaidu suka bayar da rahoton farmaki daga jirage masu saukar ungulu na Apache, lamarin da mazauna yankin suka kwatanta “da tsananin tashin hankali” a cikin birnin.

A cewar Majalisar Dinkin Duniya, kutsen Isra’ila a yankin ya turtsatsawa ‘yan Gaza miliyan guda neman mafaka a wasu wurare a yankin, inda cen din ma ba su tsira ba daga hare-hare.

Akalla Falasdinawa 37,232 ne aka kashe, akasarinsu mata da kananan yara, sannan wasu 85,037 kuma suka samu raunuka sakamakon mummunan hare-hare da sojojin Isra’ila ke kai wa zirin a yayin da aka shiga wata tara na yakin da ya barke bayan harin Hamas na ranar 7 ga watan Oktoba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments