Jami’an leken asirin Iran sun kama dan leken asirin Mossad a lardin Ardabil

Jami’an leken asirin kasar Iran sun gano tare da cafke wani mutum a lardin Ardabil da ke arewa maso yammacin kasar bisa zargin yin leken

Jami’an leken asirin kasar Iran sun gano tare da cafke wani mutum a lardin Ardabil da ke arewa maso yammacin kasar bisa zargin yin leken asiri ga hukumar leken asiri ta gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta Mossad.

Ma’aikatar leken asiri ta Iran na neman mutumin wanda ya gudu, An kama shi ne bisa umarnin ofishin mai gabatar da kara na lardin Ardabil.

A cewar ofishin yada labarai na ofishin mai shigar da kara na lardin, wakilin na Mossad yana hulda da wasu manyan jami’an leken asirin Isra’ila ta kafafen sada zumunta, kuma yana tattara musu muhimman bayanai a karkashin inuwar editan labarai.

Ya yi balaguro zuwa wasu larduna da dama, daga karshe kuma ya bar kasar, kafin a gano shi tare da kama shi a wani samame na ba-zata a lardin Ardabil.

An bayar da rahoton cewa Mossad ta yanke shawarar rufe asusun mai amfani da yake amfani shi, tare da share bayanan da ke da alaka da shi jim kadan bayan samun labarin kama mutumin.

A farkon wannan shekara, ma’aikatar leken asirin Iran ta ce dakarunta sun gano wani adadi mai yawa na ‘yan leken asirin da ke da alaka da Mossad a kasashe 28 na duniya.

Sanarwar ta kuma kara da cewa, an gudanar da wannan aiki ne bisa wasu jerin tsare-tsare na ayyukan leken asiri, da kuma yin amfani da hanyoyi daban-daban na tattara bayanan sirri, wanda ya kai ga bada damar samun nasarar cafke shi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments