Wakilin kungiyar Hamas a kasar Lebanon Osama Hamdan ya gargadi HKI idan ta ci gaba da yakin da take a gaza, mai yuwa ma fi yawan Fursinonin da ta yaki don kubutar da su, su zama gawaki.
Tashar talabijin ta Presstva nan Tehran ta nakalto Hamdan yana fadar haka a jiya litinin ya kuma kara da cewa idan Banyamin Natanyahu ya ci gaba da yaki a gaza, to zai rasa dukkan fursinonin da suke hannun kungiyar Hamas, ko kuma ba zasu taba komawa hannunsu ba har abada.
Kungiyar Hamas ta kama wasu sojoji da kuma yayudawan sahoyoniya kimani 250 a lokacinda ta farwa matsugunan yahudawa gewaye da zirin Gaza a lokacin fara wannan yakin, ya kuma kammala da cewa ya zuwa yanku hare haren sojojin yahudawan sahyoniya ya kashe kimani kasahi 70% na fursinonin da ke hannunta.
A farkon watan mayun da muke ciki ne Khalil Al-Hayya mataimakin shugaban siyasa na kungiyar Hamas ya bayyana cewa kashi 70% na fursinonin HKI wadanda suke tsare a hannun Hamas sun halaka.