Denmark, Ta Bukaci Isra’ila Ta Kawo Karshen Aikin Soji A Rafah

Ministan harkokin wajen kasar Denmark, ya bukaci Isra’ila data kawo karshen aikin soji a binrin Rafah. Furucin Lars Loke Rasmussen, na zuwa ne bayan da

Ministan harkokin wajen kasar Denmark, ya bukaci Isra’ila data kawo karshen aikin soji a binrin Rafah.

Furucin Lars Loke Rasmussen, na zuwa ne bayan da  kotun kasa da kasa ta ICJ, ta bukaci Isra’ila data dakatar da ayyukan soji a birnin Rafah da kuma bude mashigar Rafah dake kudancin zirin Gaza.

Ministan harkokin wajen Denmark din, ya bayyana cewa gwamnatin kasar Denmark ta dade tana neman tsagaita bude wuta a zirin Gaza,

Inda ya jaddada cewa: “Yanzu kuma bisa ga hukuncin da kotun duniya ta yanke, dole ne mu ga an dakatar da harin kasa da Isra’ila ke kai wa Rafah da kuma tsagaita wuta.”

Yayin da yake ishara da hukuncin da kotun kasa da kasa ta yanke na dakatar da ayyukan soji na gwamnatin sahyoniyawan a Rafah da kuma bude mashigar Rafah, ministan harkokin wajen Denmark ya ce: Dole ne dukkan kasashe su mutunta dokokin kasa da kasa, don haka Denmark na fatan Isra’ila ta yi aiki da wannan hukuncin.”

Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya da ke birnin The Hague na kasar Netherland, ta ba da umarnin dakatar da ayyukan soji na gwamnatin sahyoniyawan a birnin Rafah cikin gaggawa tare da neman a sake bude mashigar Rafah domin kai agajin jin kai a zirin Gaza.

Kasashe da kungiyoyi daban-daban na kasa da kasa da na shiyya-shiyya sun yi maraba da hukuncin kotun.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments