Sanata Rand Paul mai wakiltan Jihar Kentucky a kasar Amurka ya bayyana cewa takunkuman tattalin arziki wadanda gwamnatocin Amurka da suka shude da kuma ta yanzun suka yi ta dorawa kasashen Iran, China da kuma Rasha basu yi wani amfani ba.
Kamfanin dillancin labaran Isna na kasar Iran ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran Tass na kasar Rasha na cewa, sanata Paul ya fadi haka a lokacinda yake amsa tambayoyi dangane da ayyukan ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Amurka.
Paul ya kara da cewa, shin akwai wani jami’in ma’aikatar harkokin wajen Amurka da zai fada mani, inda takunkuman tattalin arziki ta sauya ikidar wata kasa a duniya?.
Ya kuma kara da cewa maimakon takunkuman tattalin arziki a kan wadannan kasashe, da yakamata gwamnatocin Amurka su bi hanyoyin diblomasiyya don warware matsalolinta da wadannan kasashe. Amma abin bakinciki, munayin haka tun dsa dadewa ba btare da la’akari da abinda ya dace ba.’ Sanaton ya kammala.
A wani bangare na jawabinsa Sanata paol ya kara da cewa kuskure ne gwamnatin Amurka ta yiu amfani da dukiyoyin kasar Rasha da suke kasashen ketare don aikawa kasar Ukraine makamai, don kasar Rasha ma tana iya yin hakan.
Yace akwai wasu takunkuman da gwamnatocin Amurka suka dorawa wadannan kasashe, wasu yakamata a dauke su, amma sun ci gaba da kasnacewa na tsawon shekaru 5, wasu ma an kara tsawaitasu na shekaru 10.