An Dauke Dokar Ta-Baci A Jihohi Hudu Na kasar Sudan Ta Kudu

An dauke Dokar ta baci a wasu jihohi guda 4 na kasar Sudan ta kudu bayan samun sassautawar alamura

Shugaban kasar Sudan ta Kudu, Salva Kiir ya sanya hannu a wata dokar da ta kawo karshen dokar ta-baci a jihohi hudu, a matsayin hanyar da za ta ba wa hukumomi damar sake dawo da doka da oda a wadanan yankuna.

Sanarwar shugaban kasar tana zuwa ne adaidai lokacin da ake shirin gudanar zabuka na farko a wannan kasar da ta yi kaurin suna a rashin tsaro a wasu yankuna, kusan shekaru  goma sha biyar da suka gabata.

Za  agudanar da zaben a ranar 11 ga Fabrairu, 2027,bayan dage zaben da aka tsara za’a gudanar da shi a 22 ga Disamba 2026.

Jihohin da wannan dokar ta shafa su ne Unity, Warrap, Lakes, da Western Bahr el-Ghazal. A cikin wadannan jihohi hudu dake tsakiyar da arewacin kasar, an ayyana dokar ta-baci a lokuta daban-daban don dakile tashin hankali tsakanin al’ummomi, satar shanu, da rashin tsaro.

Matakin da hukumomin suka dauka na ayana dokar ta baci ,bai yi tasiri a cewa da dama daga cikin masu lura da lamuran tsaro ba, an ci gaba da fuskantar tashin hankali a wadanan yankun,musamman a jihohin Warrap da Unity, inda aka kashe akalla mutane 70 a watan da ya gabata a rikicin da ya faru tsakanin al’ummomi a kan iyakar jihohin biyu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted