Dakarun sojin kasar yamen sun kai hare – haren ramuwar gayya guda 5 a muhimman wurare a tsakiyar kasar saudiya a matsayin martani kan hare haren da gidan sarautar kasar ke kai wa kan fararen hula da muhimman gine-gine da suka hada da tashoshin wutar lantarki a yakin da ta kaddamar akan kasar yamen.
Brigadier Janar Yahya Saree kakakin sojin kasar yamen ya sanar a daren jiya cewa dakarun sojin kasar sun kaddamar da hare hare a sa’oi 48 da suka gabata a muhimman wurare a cikin kasar saudiya domin mayar da martani kan harin da kasar saudiya ke kai wa kan fararen hula a birnin sana’a da sauran larduna a kasar yamen
Saree ya kara da cewa harin farko da aka kai ya sauka a filin saukar jiragen sama na sarki khalid dake birnin riyad, yayin da na biyun kuma ya sauka akan radar tsaro dake kudu maso yammacin kasar dake abha da kuma khamis mashait, hari na 3 kuma ya fada a matatar mai ta jazan kuma gobara ta tashi a wajen
Haka zalika Saree ya kara da cewa hari na 4 kuma ya fada a cibiyar samar da iskar gas ta hawiya dake lardin gabas a kasar ta saudiya, kudanci al-ahsa kuma gobara ta tashi a wajen, sai kuma hari na biyar inda takai a cibiyar samar a wutar lantarki ta shuqaiq da jazan kuma ya Haifar da mummunar asarar a wajen