Iran : Amurka Da Isra’ila Ne Ke Da Alhakin Kisan Yaran Minab

"Ba za mu taba mantawa da wannan mummunan harin ba," inji Pezeshkian.

Shugaban Iran Massoud Pezeshkian ya bayyana cewa Amurka da Isra’ila su ne ke da alhakin mummunan harin da aka kai makarantar firamare ta Minab da ke kudancin Iran.

Ya jaddada cewa Iran ba za ta taba mantawa da wannan mummunan harin ba, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar yara da dama, malamai, da iyaye.

“Gwamnatin Amurka da gwamnatin Isra’ila ne ke da alhakin kisan yaran Minab 168,” kamar yadda Pezeshkian ya rubuta a cikin wani sako a ranar Juma’a.

“Ba za mu taba mantawa da wannan mummunan harin ba,” inji shi.

Ya lura cewa babu wani babban abin tausayi ga uba fiye da binne yaron da ya kamata ya ci gaba da rikewa a hannunsa.

Shugaban Iran ya jaddada cewa wannan mummunan harin ya fallasa mizanin wadanda ke ikirarin kare hakkin dan adam.

A safiyar harin da sojojin Amurka da Isra’ila suka kai wa Iran a ranar 28 ga Fabrairu ne wasu makamai masu linzami guda biyu na Tomahawk sun kai hari kan Makarantar Firamare ta Shajareh Tayyebeh.

Harin ya kashe akalla mutane 155, ciki har da yara 120 ‘yan tsakanin shekaru bakwai zuwa goma sha biyu tare da malamai 26.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted