Iran: Zamu Karfafa Sojojin Ruwa da Makaman Zamani Don Kare Kasar Daga Ruwa

Ministan tsaron kasar Iran Mehrdad Akhlaghi ya bayyana cewa ma’aikatarsa zata karfafa sojojin ruwa na kasar wato Navy don basu damar kare kasar ta ruwa

Ministan tsaron kasar Iran Mehrdad Akhlaghi ya bayyana cewa ma’aikatarsa zata karfafa sojojin ruwa na kasar wato Navy don basu damar kare kasar ta ruwa musamman a dai dai lokacinda mashigar ruwa ta Hurmuz ta zama ruwa mai muhimmanci ga kasar ga kuma duniya, sannan saboda fuskantar barazanar da makiya suke wa kasar a mashigar da kuma tekun farisa gaba daya.

Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan yana fadar haka a yau Asabr 07 ga watan Aazar -1405. Ko 28-11-2026, wanda kuma it ace ranar sojojin ruwa ko Navy ta kasa.

Ministan ya kara da cewa, sojojin ruwa sun taka rawar a zo a gani a kasar tun bayan nasarar juyin juya halin musulunci a kasar a shekara 1979. Ya ce: Sojojin tare da sojojin ruwa na IRGC sun hada karfi da karfi wajen ayyukan kare tashoshin jiragen ruwa da kuma samar da zaman lafiya a wadannan yankuna nab akin ruwa na kasar tun kallafeffen yaki na farko da kuma daga baya. A halin yanzu sun maida hankalin ka kare tekun farisa da kuma musamman mashifar ruwa tahurmuz daga makiya. Da kuma tabbatar da ikon iran ya ci gaba da kasancewa a kan mashigar ruwa mai matukar muhimmanci ta Hurmuz. Yace Iran tana samar da makatanta na zamani da kuma kyautata wadanda suka tsufa gaba daya a cikin gida.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted