Hizbulla Tace Dakarun Sa Kai Ne Zasu Kawo Karshen Mamayar Isra’ila

sakataren kungiyar hizbullah ta kasar labanon yace dakarun sa kai ne zasu kawo karshen mmayar isra'ila

Babban sakatare janar din kungiyar hizbulla ta kasar Labanon shaikh Naim Qaseem ya jinjinawa namijin kokarin da dakarun sa kai  wato Basiji suke yi, kuma ya jaddada cewa tabbatar za su yi nasara kuma su ne za su kawo karshen mamayar isra’ila

shaikh naim Qasem yayi  wannan bayani ne  ajiya jumaa a wani sako da ya aike da shi ga dakarun sa kai na Basij game da tunawa da zagowar ranar da aka kafa kungiyar a ranar 26 ga watan nuwamba shekara ta 1979 bayan umarnin da jagoran juyin musulunci na iran Imam ayatollah ruhullah alkhumaini

Haka zalika ya jinjinawa dakarun na sa kai game da sadaukar da rayukansu da dikiyoyin su  da suke yi wajen ganin an samar da yancin kai da kuma kare mutuncin kasa, yace muna da dakarun sa kai,  isra’ila ba za ta ci gaba da wanzuwa a matsayinta na yar mamaya ba a kasar labanon ba,

Daga karshe yayi kira ga dukkan dakarun sa kai da su ci gaba da gudanar da ayyukansu, a lokaci guda kuma su kasance cikin shirin ci gaba da kare kasar duk lokacin da bukatar hakan ta taso

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted