Masud pezeshkiyan shugaban kasar iran ya bayyana cewa Amurka da isra’ila suke da alhakin mummunan harin da aka kai a makaranta a garin minab dake kudancin kasar iran, wanda yayi sanadiyar mutuwar yara da malamai da iyayen yara, ya jaddada cewa iran ba zata taba mantawa da wannan mummuna laifin yakin ba.
A wani bayani da ya wallafa a shafinsa na x a jiya jumaa shugaban kasar iran yace gwamnatin Amurka da ta isara’ila sune ke da alahakin kashe yara 168 a makarantar firamare ta minab , kuma ba za mu taba mantawa da shi ba. yace babu wani abin da ya fi zafi a zuciya mahaifi ya bizne dansa da ya zama dole ya rike kafadunsa
A cikin sao’in farko na ranar 28 ga watan fabareru ne ,ranar farko da amurka da isra’ila suka kaddamar da harin soji akan kasar iran, inda ta harba manyan manyan makamai masu linzami na tomahawk a makarantar shajare dayyibe, inda aka kalla ta kashe mutane 155 wanda 120 daga cikinsu yara kana na ne da basu wuce shekaru 7 zuwa 12 ba, haka kuma malamai mata guda 26 suka yi shahada
Mataimakin shugaban kasar iran kan harkokin shari’a majid Ansari ya fadi a makon da ya gabata cewa kasar ta fara daukar matakin shari’a a amurka da kasashen turai guda 4, dangane da harin makami mai linzami da Amurka ta kai a kan makarantar Minab