Sanata A Amurka Ta yi Kira Ga Majalisar Ta Dakatar Da Bada Kudade

wata sanata a amurka ta yi kira ga majalisar dokoki da ta dakatar da bada kudade ga gwamnati da take amfani da su wajen yakar

Sanata Tammy Duckworth ta yi  kira ga majalisar dokokin amurka da ta yanke dukkan kudade da take bawa gwamnatin trump game da yakin da ya karya doka da take yi da kasar iran, kuma ta tilasatawa shugaban kasar Donald trump kawo karshen yakin cikin gaggawa

Haka zalika yar majalisar  ta sha bayyana yakin da Amurka da gwamnatin isra’ila suka kaddamar kan kasar iran a ranar 28 ga watan fabareru a matsayin wanda ya sabama kundin tsarin mulki da ya janyo musu bala’I da majalisar ba ta amince da shi ba

Tace zamu kada kuri’ar nuna kin amincewa da duk wani kudi da gwamnati ta bukata da bai kunshi yin kwaskwarima kan kudin da zaa yi amfani  da shi wajen daukar mataken soji  kan kasar iran ba, har zai ya samu izinin majalisar a hukumance

Masu suka sun bayyana cewa ya zuwa yanzu yakin ya lakume biliyoyin daloli, yayi sanadiyar mutuwa da raunata sojoji da dama , ya sanya matsin lamba kan kayan aikin soji na ruwa, tare da haifar da hauhawan farashin makamashi ga marasa karfi a amurka, amma duk da haka ba’a cimma manufofin da Washington ta bayyana tana son cimmawa ba a yakin ta da iran

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted