Duk da cewa kasashen kungiyar Sahel ta AES, wato Mali, Burkina Faso, da Jamhuriyar Nijar, sun fice daga kungiyar ECOWAS a hukumance tun a watan Janairun 2025, sun hada kai da wasu kasashen yammacin Afirka 12 wajen shiga wani babban shirin noman shinkafa na dala miliyan
Wannan shiri mai suna REWARD-ECOWAS, wanda kungiyar ECOWAS ta ƙaddamar tare da haɗin gwiwar Bankin Raya Afirka da cibiyar AfricaRice, na da nufin rage dogaron yankin kan shinkafar waje da kuma tabbatar da wadataccen abinci nan da shekarar 2035.
Kodayake kasashen na Sahel sun jaddada cewa babu ja da baya a game da ficewarsu daga ECOWAS, shigarsu wannan shiri na nuna yadda bangarorin biyu ke cigaba da haɗin kai a fannoni masu muhimmanci.
Kasancewar kasashen kungiyar AES a cikin wadanda za su ci gajiyar wannan shiri na zuwa ne kusan shekaru 2 bayan ficewar da suka yi daga ECOWAS, wanda ta fara aiki a ranar 29 ga watan Janairun 2025.