Rahotanni sun bayyana cewa kwamandan dakarun sojan ruwa na kasar ian Real admiral shahram irani, ya bayyana cewa tashar jiragen ruwa na kasar suna gudanar da ayyukan su kamar yadda suka saba kuma ana ci gaba da kokarin karya killacewar da amurka ta yi musu ta ruwa, kuma ya jaddada cewa tashar jiragen ruwa ta kasar iran ba za ta taba daina aiki ba duk da yukurin da amurka ke yi na kassarata ta fuskar tattalin arziki
Kwamandan yayi wannan bayani ne a wata hira da gidan talabijin na kasa yayi da shi a daren jiya jumaa’a kuma yayi watsi da jita-jitar da makiya suke yadawa game da yanayin da tashar jiragen ruwa ta kasar iran ke ciki.
Hakazalika ya kara da cewa a aladance an sanya takunkumin ruwa tun kafin fara yaki domin matsin lamba ga makiya, sai dai sanar da wannan takunkumin a yayin da ake yaki tamkar tabbatarwa ne cewa makiya sun kasa cimma manufofinsa na soji, domin makiya basu cimma ko da daya daya cikin manufofinsuba
kwamandan ya kara da cewa dakarun sojan ruwa na kasar iran sun samu nasarar takawa makiya burki da hana su matsawa ko ina acikin teku, inda suka nisanta su zuwa wuri mai nisa a bangaren tekun larabawa da kuma tekun kudancin indiya