Hukumar yansandan ciki ta Amurka (FBI) ta bada sanarwan cewa an kai mata hare hare ta yanar gizo a karo na biyu, kuma a wannan karon sun sace bayanai na ma’aikatan hukumar na da da na yanzu.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto tashar talabijan ta CNN na fadar haka ta kuma kara da cewa wannan shi ne karo na biyu Kenan da masu kai hare hare na yanar gizo suke farwa kayakin aikin na lantarki na hukumar a cikin wannan shekara.
Labarin ya kara da cewa a cikin watan satumban da ya gabata an kai mata hare hare irin wannan inda suka sace bayanin masu muhimmanci na hukumar wadanda suka hada da sammaci asalin dangantakan mutane. Bayanin ya kara da cewa wadanda suka kai hare haren sun rubuta a bakin shafinsu kan cewa sune “ShinyHunters” kuma sun kaiwa FBI farmaki ne don sun bada sanarwa ga kamfanoni kada su biya kudade ga wadanda suka kai masu hare hare ta yanar gizo.
Kasashen Turai da Amurka dai suna ta fama da hare haren yanar gizo a cikin watannin da suka gabata, wasu kasashen turai sun zargi Iran ta kai masu irin wadan nan hare hare.