Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran ya bayyana cewa: Kokarin cimma yarjejeniya mai kyau da daraja shi ne zai kiyaye mutuncin Iran
Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Iran ba zata yarda da yanayin yaƙi ko zaman lafiya ba, kuma tana da yakini da buƙatar kawo ƙarshen wannan yanayi. Ya bayyana cewa domin kasar ta tsira daga wannan yanayi, tana da zaɓuɓɓuka biyu kawai: yaƙi ko zaman lafiya, kuma babu wanda ke goyon bayan yaƙi. Saboda haka, mafita tana nan a kan cimma yarjejeniya.
Da yake magana game da shawarar da aka gabatar a cikin kwanaki biyu da suka gabata, Araqchi ya ce wannan shawara tana nan a kan teburi, kuma idan Amurkawa da gaske suna son cimma yarjejeniya, wannan shawara za ta iya share fagen cimma yarjejeniya mai faɗi.
Ministan Harkokin Wajen Iran ya yi watsi da ikirarin cewa: Iran na da niyyar kai hari kan Amurka da bam mai guba ko kashe shugabanni, kuma Iran ta ɓoye makamai masu linzaminta a ƙarƙashin madatsun ruwa, yana mai cewa irin waɗannan maganganun ba za a yarda da su ga al’ummar Amurka ba, ba wai kawai shugabannin siyasa ba. Ya nuna cewa Fira Ministan Haramtacciyar Kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu, wanda yake ganin rayuwarsa ta siyasa wajen sake farfaɗo da yaƙi da Iran, yana kan wannan mummunan ra’ayin.