Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Esmail Baghaei ya bayyana cewa, labaran da wasu jami’an gwamnatin kasar Amurka suka fara yadawa na cewa Iran tana kokarin mallakar makaman guba da kuma sinadarai babban karya ce.
Baghaei ya bayyana haka ne a yau Jumma’a a shafinsa na X, ya kuma kara da cewa, da farko suna zargin Iran da kokarin mallakar makaman Nukliya, a yanzun kuma sun sauya zuwa makaman guba da kuma na sinadarai masu cutarwa. Ya ce iran wannan karyar ba saboda bane, don bai kamata Amurka su dauki cewa duniya ta manta da karyar da suka yi dangane da yaki kan kasar Iraki. Sun manta da cewa sakataren harkokin wajen Amurka na lokacin Colin Powell ya je kwamitin tsaro na MDD ta bayyana cewa gwamnatin kasar Iraqi ta na kokarin mallaka ko kuma ta mallaki makaman kare dangi, amma a lokacinda suka mamaye Iraki suka nemi makaman suka rasa. ?.
A lokacin gwamnatin Amurka ta yi karya don ta sami goyon bayan mutanen kasar na shiga yaki a kasar Iraki, amma bayan mamaya mun ga yanda mamayar Iraki ya zama musiba ba ga kasar Irakawa kadai ba ba kuma makobta kadai ba, har da sojojin Amurka sun mutu a wannan yakin da kuma mamayar.