Kakakin sojojin kasar Yemen Burgedia Janar Yahyah Saree ya bada sanarwan bukatar sojojin kasars wajen da suke a tashar jiragen sama na birnin Aden a kudancin kasar su fice daga tashar da gaggawa, saboda samuwar jirgin yakin dakon kaya na kasar saudia a tashar dauke da makamai zuwa sojojin hayarta.
Tashar talabijan ta Almayadeentv ta kasar Lebanon ta nakalto sanarwan daga bayanin da Saree ya fitar a dazu dazun nan wanda yake kira ga dukkan wadanda suke cikin tashar su fice saboda kada makaman gwamnatin kasar su rutsa da su a cikin tashar.
A wani labarin kuma jiragen yakin kasar Saudia sun kai hare hare har guda 4 a kasar ta Yemen a yau Laraba, inda suka yi luguden wuta a kan ginin jami’an tsaro a yankin Makhaa da ke cikin lardin Ta’aiz na bakin ruwa. Hakama jiragen yakin na Saudia sun kara hari kan hasumiyar sadarwa ta Jabal Habashi shi ma a cikin lardin Ta’aiz. Sannan a lardin Lahij kuma sojojin haya na kasar ta Saudia sun kai hare hare kan gidajen mutane inda wutansu ya sami yara kanana guda biyu. Sannan a lardin Umran kuma jiragen saudia sun kai hare hare har guda 7 .Gwamnatin kasar ta Yemen ta bayyana cewa, a cikin sa’o’ii 24 da suka gabata jiragen yakin saudia sun kai hare hare har sau 81 a duk fadin kasar.