Iran: IRGC ta Hari Sansanonin Amurka A Yammacin Asia

Dakarun kare juyin juya halin musulunci na kasar Iran sun kai hare haren maida martani kan sansanonin sojojin Amurka da dama a yankin karkashin farmaki

Dakarun kare juyin juya halin musulunci na kasar Iran sun kai hare haren maida martani kan sansanonin sojojin Amurka da dama a yankin karkashin farmaki wanda aka sanya masa suna “Nasr 2”, wanda da suka hada da Kuwait, Bahrai da kuma Jordan.

Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto rundunar tana fadar haka a yau Alhamis kan cewa,  a hare haren har zagaye na 4, sun cilla makamai masu linzami kan cibiyar tallafawa sojojin Amurka da ke tashar jiragen ruwa na Abdullahi a kasar Kuwait, sai kuma hare hare zagaye na 5 wadanda suka fada kan cibiyar bada umurni da rumbun ajiyar makamai da wasu kayakin soje a sansanin sojojin ruwa na Amurka mafi girma a yankin a yankin yammacin Asia da ake kira ‘5th da ke kasar Bahrain.

Labarin ya kara da cewa, wasu hare hare har guda 6 sun fada kan sansanin sojojin sama na Amurka wanda ake kira Al-Azraq dake kasar Jordan, inda suka larata wuraren ajiyar jiragen yakin Amurka smfurin F35 da dama da kuma wasu jiragen yaki wadanda ake sarrafasu daga nesa samfurin MQ 9.

Sun abubuwan da aka lalata a sansanin Al-Azraq sun hada da na’irorin sadarwa na & mai amfani da tauraron dan’adam, garkuwan makamai masu linzami da rada radarsu, da wuraren cilla makamai masu linzami masu suna HAMARS na Amurka a kasar Kuwait.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted