Kakakin Majalisar Dokokin Iran Ya Gargadi Amurka Da Ta Rufe Bakinta Ko Ta Biya Farashin Saba Alkawari Da Ta yi.

Kakaki majalisar dokokin kasar iran Mohammad Qalibaf ya gargadi Amurka cewa akwai bukatar ta mutunta alkwuran da ta dauka ko kuma ta biya farashin keta

Kakaki majalisar dokokin kasar iran Mohammad Qalibaf ya gargadi Amurka cewa akwai bukatar ta mutunta alkwuran da ta dauka ko kuma ta biya farashin keta yarjejeniyar dakatar da yaki da aka cimma  da kasar Pakistan ta shiga tsakani

Qalibaf ya rubuta a shafinsa na X a yau lahadi bayan da kasar Amurka ta kaddamar da hari karo na 3 a kasar iran da ya keta yarjejeniyar fahimtar juna da aka sanyawa hanun tsakanin Tehran da Washington, yayi ishara da lambar 5 na yarjejeniyar da ta nuna cewa iran ce za ta tsara yadda za’a bude mashigar Hurmuz wajen bincike mai muhimmanci na makamashi

A matsayin mayar da martani kan harin baya bayan nan da Amurka ta kai a kudancin kasar iran, dakarun tsaron iran sun kaddamar da hari da makamai masu linzami da jiragen sama mara matuki a kan sansanin sojojin Amurka dake kasashen Jodan, Kuwair, da kuma kasar Baharain

tuni dai dakarun kare juyin musulunci na kasar iran suka sanar da rufe mashigar Hurmuz  har sai baba ta gani  saboda kokarin da aka yi na yin amfani da wajen ba bisa ka’ida ba akan jirgen ruwa dake dakon kwantenoni. don haka za ta ci gaba da kasancewa a rufe  har sai Amurka ta kawo karshen katsalandam din da take yi a yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted