Qalibaf Ya Ce: Al’ummar Iran Ba Zasu Amince Da Tattaunawa Karkashin Barazana Ba

Kakakin Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya jaddada cewa: Ba za su taba yarda da tattaunawa ba a ƙarƙashin barazana Kakakin Majalisar Shawarar Musulunci wato

Kakakin Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya jaddada cewa: Ba za su taba yarda da tattaunawa ba a ƙarƙashin barazana

Kakakin Majalisar Shawarar Musulunci wato Majalisar Dokokin Iran Mohammad Baqir Qalibaf ya bayyana cewa: Shugaban Amurka Donald Trump yana da niyyar mayar da teburin tattaunawa zuwa teburin mika wuya, yana mai jaddada cewa: “Iran ba zata taba yarda da tattaunawa a karkashin barazana ba.”

Qalibaf ya rubuta a cikin wani sako a dandalin sada zumunta na X da sanyin safiyar ranar Talata cewa: “Trump, ta hanyar sanya takunkumi da karya yarjejeniyar tsagaita wuta, yana son mayar da teburin tattaunawa zuwa teburin mika wuya, bisa ga rudun tunaninsa, ko kuma ya ba da hujjar sake barkewar rikici.”

Shugaban Majalisar Dokokin Iran ya tabbatar da cewa: “Iran ba zata taba yarda da tattaunawa a karkashin barazana ba, kuma ya kamata a lura cewa: Yarjejeniyar tsagaita wuta da aka sanar tsakanin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da Amurka da Isra’ila a ranar 8 ga Afrilu ta kasance na tsawon makonni biyu ne, da nufin samar da dama don nemo hanyoyin diflomasiyya don kawo karshen yakin da ya kunno kai.

Kwanaki uku bayan haka, an yi tattaunawa tsakanin Iran da Amurka a ranar Asabar, 11 ga Afrilun wannan shekara a birnin Islamabad na Pakistan, tsakanin tawagar Iran karkashin jagorancin Mohammad Baqir Qalibaf, Shugaban Majalisar Dokokin Iran, da kuma tawagar Amurka karkashin jagorancin J.D. Vance, Mataimakin Shugaban Amurka Trump.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted