‘Yar majalisar wakilai daga jam’iyyar Democrat ta kasar Amurka Ilham Omar ta bayyana cewa jami’an tsaro a jawabin ‘ the State of the Union address’ wanda shugaban kasar Amurka Donal Trump yayi a jiya Laraba, sun fidda bakuwarta da karfi daga zauren jawabi sannan sun tsare ta.
Mujallar ‘The Nation’ ta kasar Amurka ta nakalto Omar tana fadar haka, ta kuma kara da cewa jami’an tsaron basu da hurumin yiwa bakonta haka. Umar dai tana wakiltan jihar Minnisota ne a majalisar wakilan kasar Amurka. Sannan ta zo da Aliya Rahman diyar shekara 43 a duniya a zauren taron inda shugaban yayi jawabi, saboda abin da jami’an tsaro shige da fice na Amurka suka yi mata a birnin Minnieapolis a ranar 12 ga watan Jenurun da ya gabata, inda suka fidda ita da karfi daga motarsa sannan suka tsareta na wani lokaci saboda wai ta zagi wani jami’in tsaro.
Ilham tace a lokacin Jawabin Trump a jiya Aliya Rahma ta tashi ta tsaya na minta daya saboda nuna takaicinta a gaban Trump kan abinda Jami’an tsaronsa suka yi mata. Amma sai jami’an tsaron Trump a zauren suka fidda ita suka kuma tsare ta.