Matakan Isra’ila a Yammacin Kogin Jordan na Nufin Tilasta Korar Falasdinawa (MDD)

Majalisar Dinkin Duniya, ta bayyana cewa matakan Isra’ila a yammacin Kogin Jordan na da nufin tilasta korar Falasdinawa daga yankunansu. Mai Magana da yayun hukumar

Majalisar Dinkin Duniya, ta bayyana cewa matakan Isra’ila a yammacin Kogin Jordan na da nufin tilasta korar Falasdinawa daga yankunansu.

Mai Magana da yayun hukumar kare Hakkin Dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya Ravina Shamdasani ta bayyana matukar damuwa game da fadada ikon Isra’ila a Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye.

Shamdasani ta bayyana a wani taron manema labarai na baya-bayan nan cewa wadannan matakan an yi su ne kai tsaye don sauƙaƙe korar Falasdinawa daga yankunansu ta hanyar kirƙkirar yanayi mai tsauri ga mazauna.

A cewarta shawarar Isra’ila na fadada ayyukan sa ido da iko a yankunan da ke ƙarƙashin Hukumar Falasdinawa ya haifar da damuwa mai tsanani game da shari’a da kare hakkin dan adam.

Shamdasani ta yi gargaɗin cewa waɗannan matakan Isra’ila suna hanzarta aiwatar da wani tsari da ke haifar da mamaye kasar Falasdinawa ba bisa ƙa’ida ba, wanda hakan ya saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa. Ta yi ikirarin cewa waɗannan manufofi suna nufin canza matsayin shari’a na Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye domin tilasta wa Isra’ila ikon mallakar yankin na dindindin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted