Mahukuntan Iran sun jaddada cewa: Ci gaba da tace sinadarin Yuranium ba zai taba shiga cikin ajandar kowace tattaunawa ba
Wata majiya mai tushe daga Iran ta shaida wa tashar talabijin ta Al-Alam cewa: Ci gaba da tace sinadarin yuranium a kowace tattaunawa ja ne ga Iran.
Majiya ta bayyana cewa: Amurka ta nemi a mayar da tattaunawar daga Muscat zuwa Geneva, tana mai jaddada cewa Iran ba ta damu da rage damuwar wasu kasashe game da karfin makamanta masu linzami ba.
Ta kuma lura cewa Amurkawa ba su tada batun kare hakkin dan adam kwata-kwata ba, tana mai cewa, “Iran ta shiga tattaunawar makamashin nukiliya ne don dage takunkumai, kuma ba ta damu da barazana ba.”
A cewar ma’aikatar harkokin wajen Iran, Ministan harkokin wajen kasar Abbas Araqchi ya yi tafiya zuwa Switzerland a matsayin shugaban tawagar diflomasiyya don gudanar da zaman zagaye na biyu na tattaunawar nukiliya.
Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta fayyace cewa: Za a gudanar da tattaunawar nukiliya ba ta kai tsaye ba da Amurka a ranar Talata, karkashin jagorancin Masaurantar Oman. Ta kara da cewa: Minista Araqchi zai gana a Geneva da takwarorinsa na Switzerland da Oman, da kuma Darakta Janar na Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Duniya.