Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Ya Ce: Babu Batun Yaki Tsakanin Amurka Da Iran

Ministan harkokin wajen Turkiyya ya bayyana cewa: Babu wata alama da take gwada alamar bullar yaki tsakanin Amurka da Iran Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan

Ministan harkokin wajen Turkiyya ya bayyana cewa: Babu wata alama da take gwada alamar bullar yaki tsakanin Amurka da Iran

Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya tabbatar da cewa: Yankin a halin yanzu bai nuna wata alama ta wani yaƙi da ke shirin faruwa tsakanin Amurka da Iran ba, wanda hakan ke nuna cewa ɓangarorin biyu sun shirya tattaunawa da ci gaba da neman fahimtar juna.

A wata hira da ya yi da gidan talabijin na CNN Turk, Fidan ya ce, “Batun Iran yana da matuƙar muhimmanci a cikin ajandar diflomasiyyar Turkiyya. Yankin ya gaji kuma ba zai iya jure wani rikici ba. Saboda haka, Turkiyya tana amfani da duk hanyoyin da ake da su don hana duk wani tashin hankali na soja.”

Ministan Turkiyya ya lura cewa: Ankara tana sa ido sosai kan ci gaban diflomasiyya tsakaninta da Iran, yana mai nuni ga wani taro da aka gudanar a Oman wanda ya haɗa wakilai daga ɓangarorin biyu. Bayan wannan taron, an yi wa jami’an Turkiyya bayani game da cikakkun bayanai game da tattaunawar daga ministocin harkokin wajen ƙasashen biyu.

Fidan ya jaddada cewa: “Muhimmin saƙon yana cikin bayyananniyar magana da ɓangarorin biyu suka yi na sha’awar ci gaba da tattaunawa,” ya ƙara da cewa, “Duk da cewa ana buƙatar hanyar sassauci da kirkire-kirkire ga tsarin tattaunawa, ba a ga wata alama a wannan matakin na shirye-shiryen zaɓin soja ba.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted