Ana Zaman Dar-dar Na Yiyuwar Barkewar Fada A Tsakanin Kasashen Habasha Da Eritrea

A wani gargadi mafi tsanani da mahukuntan kasar Habasha su ka fitar, sun yi kira ga makwabciyarsu Eritrea da ta janye sojojinta daga cikin kasar

A wani gargadi mafi tsanani da mahukuntan kasar Habasha su ka fitar, sun yi kira ga makwabciyarsu Eritrea da ta janye sojojinta daga cikin kasar cikin gaggawa.

Dama dai kasashen biyu a baya kasa daya ce, da dade da yin tsami.

A cikin watannin bayan nan kuwa, Addis Ababa ta zargi Eritrea da cewa tana goyon bayan ‘yan awaren kasarta, sai dai Asmara ta sha kore gaskiyar wannan zargi.

Ministan harkokin wajen kasar Habasha Gedion Timothewos ya aike wa da takwaransa na Eretria wasika da a ciki yake cewa:

” Abubuwan da suke faruwa a cikin kwanakin bayan nan suna nuni da yadda Eritrea ta zabi hanyar rikici.”

Haka nan kuma ya kira yi Asmara da ta janye sojojin nata daga cikin kasar Habasha,sannan kuma ta daina taimakawa kungiyoyin ‘yan aware.

Ministan harkokin wajen na kasar Habasha ya kuma ce, yadda sojojin na Eritrea su ka kutsa cikin iyakokin arewa maso yammacin kasar tasa, da kuma kai hare-hare na hadin gwiwa, ya fi karfin a kira shi tsokana, kai wa kasa hari ne.”

Sai dai kuma ministan harkokin wajen na kasar Habasha ya kara da cewa; Duk da halin da ake ciki na tsokana, ya yi Imani da cewa za a iya warware matsalar ta hanyar diplomasiyya.”

Haka nan kuma ya ce idan mu ka sami kyakkyawan jawabi daga Eritrea akan bukatunmu da suke halartattu, to a shirye muke mu bude tattaunawa cikin kyakkyawar niyya.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted