Shugabannin kasashen dake mambobi ne a kungiyar raya tattalin arzikin yammacin Afrika ECOWAS, sun sake jaddada aniyarsu ta hada kai don rubanya kokarinsu wajen yakar ta’addanci da sauran matsaloli na tsaro da yankin ke fuskanta.
Shugabannin Kasashen Ghana da Liberia da Sierre Lenone, da kuma wakilai daga Burkina Faso da Mali da Mauritania da Najeriya da Senegal da kuma Togo, sun sha alwashin sake hada kan su don tunkarar matsalolin ta’addanci da ake fuskanta a yammacin Afrika.
Shugabannin sun bayyana haka ne bayan kammala taronsu a Accra, wanda shugaba John Dramani Mahama na Ghana da Julius Maada Bio na Sierra Leone, da takwaransu na Liberia Joseph Boakai suka jagoranta.
Shugabannin sun kuma amince su rika gudanar da taruka akai-akai don duba irin ci gaban da ake samu a fannin tsaro, tare da yin musayar bayanai a tsakaninsu, baya ga karfafa dokoki na kan iyaka.