kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Qatar Majed Al-ansari ya fadi cewa tattaunawar da ake yi ta siyasa tsakanin Iran da sauran masu ruwa da tsaki a yankin a kokarin da ake yi na hana ci gaba da tada tashin tashina a tsakanin Amurka da kawayenta.
haka zalika ya kara da cewa tataunawar za ta gudana ce da mayan jami’ai da ya hada tsakanin sarkin kasar Qatar da shugaban kasar Iran da kuma ta hanyar ziyara da sadarwa da manyan jami’an kasar Qatar suka yi. dukkan wadannan ganawar ana yi su ne domin hana Afkuwar tashin hankali a yanki
kasar Qatar tana da danganta da kasashen dake makwabtaka da ita da suka hada da kasashen turkiya, Masar, Oman da kuma kasar Saudiya a wani bangare na kokarin da take yi don hana afkuwar tashin hankali
tuni kasar iran ta bayyana cewa duk wani wuce gona da iri daga Amurka to zai fuskanci mayar da martani mai tsanani ,kuma ta bayyana aniyarta na ganin an warware takaddamar ta hanyar tattaunawa da kuma diplomasiya