Iran Ta Mikawa Sojojin Kasar Karin Jiragen Yaki Wadanda Ake Sarrafasu Daga Nesa Har Guda 1000

Sojojin kasar Iran sun karbi karin jiragen yaki wadanda ake sarrafasu daga nesa ko Drones dubu guda don karfafa sojojin kasar ta sama da kasa

Sojojin kasar Iran sun karbi karin jiragen yaki wadanda ake sarrafasu daga nesa ko Drones dubu guda don karfafa sojojin kasar ta sama da kasa da kuma ruwa.

Wannan yana daga cikin shirin kasar na karfafa karfin sojojin kasar na makaman zamani, wanda yafi dacewa da a irin wannan yakin.

Kafin haka dai shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bayyana cewa, jirgin yaki mai dakon jiragen sama Armada ya kama hanya zuwa yankin tekun farisa sannan washinton tana kallon duk abinda Iran take yi, banda haka ya kara da cewa farmaki kan kasar yana daga cikin zabin da yake da shi.

Sai dai gwamnatin kasar Iran ta kara jaddada cewa a shirye take ta maida martani mai tsanani kan wanda ya takaleta da yaki. Duk da cewa kofar diblomasiyya mai ma’ana a bude take.

Major General Amir Hatami yace sojojin kasar sun ware wasu makamai masu muhimmanci don amfani da su a duk yakin da zai iya tasowa tsakanin kasar Iran da Amurka da kuma kawayenta na kusa da nesa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted