Amurka Ta Dorawa Shugaban Majalisar Koli Ta Tsaron Kasar Iran Takunkuman Tattalin Arziki

Ma’aikatan baitul mali Amurka ta dorawa Dr Ali Larijani babban sakataren hrkokin tsaron kasar Iran takunkuman tattalin da kuma wasu kwamandojin sojojin kasar. Kamfanin dillancin

Ma’aikatan baitul mali Amurka ta dorawa Dr Ali Larijani babban sakataren hrkokin tsaron kasar Iran takunkuman tattalin da kuma wasu kwamandojin sojojin kasar.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto sakataren baitul malin Amurka Scott Bessent yana fadar haka a jiya Alhamis ya kuma kara da cewa, sun dorawa wadan nan  jami’an tsaron kasar Iran takunkuman ne don abinda ya kira kare hakkin bil’adama a kasar Iran. Bessent ya ce wai gwamnatin Amurka tana goyon bayan mutanen kasar Iran.

A cikin makon da ya gabata ne kasashen Amurka da HKI suka shigo da yan ta’adda wadanda suka zo da makamai suka kashe Mutane wadanda basu san  hawa ko sauka ba. Hakama jami’an tsaro na yansanda da kuma masu sa kai na basij . sannan sun kona masallatai, alkur’ani da wurare masu tsarki da dama da suke kasar Iran.

Abin yake kasa a halin yanzu dai shi ne zaman lafiya ta dawo a mafi yawa kodukkan yankunan kasar Iran. Wadan nan makiya sun kasa cimma manufofinsu.

Amma a nashi bangare kuma Dr Larijani shugaban majalisar koli ta tsaron kasar Iran y ace Iran ba zata yi kasa a guiwa ba kan duk wani barazana kan tsaron kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted