Amurka Ta Sanya Kungiyar ‘Yan Uwa Musulmi a jerin “Kungiyoyin Ta’addanci”

Amurka ta ayyana rassan kungiyar ‘Yan Uwa Musulmi a kasashen Masar, Jordan, da Lebanon a matsayin “kungiyoyin ta’addanci na kasashen waje”, matakin da Tuni gwamnatin

Amurka ta ayyana rassan kungiyar ‘Yan Uwa Musulmi a kasashen Masar, Jordan, da Lebanon a matsayin “kungiyoyin ta’addanci na kasashen waje”, matakin da Tuni gwamnatin Alkahira ta yaba da matakin.

“Amurka za ta yi amfani da duk hanyoyin da ake da su don hana wadannan rassan ‘Yan Uwa Musulmi albarkatun da ke ba su damar aiwatarwa ko tallafawa ayyukan ta’addanci,” in ji Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio a cikin wata sanarwa.

Kungiyar ta ‘yan Musulmi ta yi tir da matakin tana mai cewa “Wannan sakamakon matsin lamba ne daga kasashen waje, musamman Hadaddiyar Daular Larabawa da Isra’ila,” kum atunbi ta ce zata  kalubalanci shawarar Amurka a kotu.

Masar, inda aka kafa kungiyar ‘Yan’uwa Musulmi a shekarar 1928, ta yi maraba da shawarar Amurka, inda ta kira da “mataki mai tsauri” a yakin da ake yi da “tsattsauran ra’ayi.”

A cikin wata sanarwa, Alkahira ta bayyana cewa wannan sanarwar ta nuna “hadarin da wannan kungiya da akidarta ta tsattsauran ra’ayi da kuma barazanar da take yi wa tsaro da kwanciyar hankali na yanki da na duniya.”

Sanarwar da Fadar White House ta fitar ta lura cewa rassan kungiyar ‘Yan’uwa Musulmi a Lebanon, Jordan, da Masar “suna aiwatarwa, karfafawa da kuma tallafawa wargaza tashin hankali da zaman lafiya da ke cutar da yankunansu, ‘yan Amurka, ko muradun Amurka.”

Ma’aikatar Baitulmalin Amurka ta tabbatar da cewa rassan kungiyar ‘Yan’uwa Musulmi na Masar da Jordan suna ci gaba da alaka da kungiyar Hamas wacce ta kai hari a ranar 7 ga Oktoba, 2023, kan Isra’ila, ‘Yan’uwa Musulmi sun haɗu da ƙungiyar Shi’a mai goyon bayan Iran Hezbollah don sannan kuma reshen kungiyar a Lebanon ya “yunkura don yin hadin gwiwa da kungiyar Hezbollah da Hamas,” in ji Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka a cikin sanarwar manema labarai.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted