Jaridar ‘Times of Israel’ ta bada labarin cewa gwamnatin Benyamin Natanyahu tana shirin sake komawa yaki a Gaza a cikin watan Maris mai zuwa a dai-dai lokacinda sojojin HKI suke matsawa layin fatse-faste wanda Trump ya shata a gaza zuwa yamma ta bakin tekun medeteranian.
Kafin haka dai a cikin watan Octoban shekarar da ta gabata ce, shugaban Amurka Donal Trump a wani shirin tsagaita wuta mai abubuwa 20 ya shata layin ruwan dorowa a gaza wanda ya bawa sojojin yahudawa iko da fiye da rabin Gaza, wanda kuma ya taso daga arewacin yankin zuwa kusa da mashigar yankin ta Rafah.
Banda rashin cika alkawalin da ta dauka a yarjeniyar Trump gwamnatin Natanyahu bata daina kai hare-hare kan Falasdinawa a gaza ba, ko da na kwana guda.
Banda haka ayyukan da sojojin yahudawan suke yi a cikin gaza yana nuni da cewa sun dawo cikin gaza ne.
Tun lokacin da aka fara abinda suka kira tsagaita wuta a Gaza, sojojin yahudawan sun kashe falasdinawa 439 a cikin watanni 3 da suka gabata, sannan sun kai hare-hare har 1,200 wadanda suka hada da jiragen yaki, makaman igwa, ko tare da tankuna yaki da sauransu.
Kungiyar Hamas dai sun ta ce yahudawan sun ci gaba da sabawa yarjeniyar tsagaita wutar, daga ciki har da hana shigowar kayakin abinci da magunguna da bukatun yau da kullum na falasdinawa fiye da miliyon biyu a yankin.