Dubban alummar kasar moroko ne suka yi gangami a gaban majalisar dokokin kasar inda suka kona tutar Isra’ila kuma suka bukaci a yanke duk wata alaka da ita kuma su goyi bayan gwagwarmayar neman yanci da alummar falasdinu ke yi.
Yan gwagwarmaya dake da alaka da kungiyar kare hakkin falasdinawa ne suka jagoranci jamaa inda suka yi gangami a gaban majalisar dokin kasar a birnin Rabad babban birnin kasar domin nuna goyon bayansu ga alummar falasdinu da kuma nuna adawa da zaluntar falasdinawa da HKI ke yi , da kuma nuna adawa da alakar dake tsakanin ribad da tal aviv.
Har ila yau sun daga kwalaye da a jiki aka rubuta kulla alaka da isra’ila taimaka mata ne wajen kisan hare dangi da take yi a gaza ,alummar maroko da hadin kan alummar musulmi zasu ci gaba da gwagwarmaya wajen tunkarar Azzalumai har sai an lalata dangantakar dake tsakani.
Duk da kulla danganta da kasar moroko ta yi da HKI amma ake gudanar da zanga-zangar nuna adawa da kuma nuna goyon bayan Alummar falasdinu da gwagwarmayar da suke yi ta kwatar yanci.