Rahotanni sun bayyana cewa a lokacin da yake ganawa da mutanen Qum da suka kai masa ziyara , jagoran musulunci na iran Ayatullah imam khamna’i da yake tsokaci kan zanga-zanga da aka yi a wani bangaren na kasar iran, yace masu zanga-zangar suna yi ne don burge wani mutum daya wato shugaban Amurka Donald Trump wanda ya kasa warware matsalar masu zanga-zangar neman hakki a kasarsa.
Yace Trump yace idan gwamnati iran ta dauki mataki akan masu zanga-zanga zasu taimakesu, wato za ta taimakawa tada hankali da cutar da alummar kasar, don haka suna yi ne saboda da shi, amma gara yaje yaji da kasarsa da ya fiye masa.
Har ila yau ya kara da cewa hannayen Trump ya riga ya gurbata da jinanan dubban alummar iran, a lokacin yakin kwanaki 12 dubban alummar kasar da janarori da masana ilimin kimiya ne suka yi shahada, sakamakon harin da ya ce shi ne ya bada umarnin aka kai, sai gashi wannan mutumin ne wai yake nuna yana tare da alummar iran.
Daga karshe yayi gargadin cewa karshen kasashe ma’abota girman kai na duniya a tsawon tarihi da suka hada shugaban Amurka Donald Trump shi ne faduwa kasa, don haka jagoran juyin musulunci ya bukaci Alummar Iran musamman matasa da su hade kansu yadda zasu sha gaban makircin makiya.