Guinea: Mamadi Doumbouya ya lashe zaben shugaban kasa tun a zagaye na farko

Hukumar zabe a kasar Guinea, ta sanar da Janar Mamadi Doumbouya a matsayin wanda ya lashe zaben shugabancin kasar tun a zagaye na farko, da

Hukumar zabe a kasar Guinea, ta sanar da Janar Mamadi Doumbouya a matsayin wanda ya lashe zaben shugabancin kasar tun a zagaye na farko, da kashi 86.72% na kuri’un da aka kada, shekaru hudu bayan juyin mulkin da ya kawo shi kan mulki.

‘Yan takara hudu sun riga sun amince da shan kaye kuma sun taya Mamadi Doumbouya murna lokacin da aka sanar da sakamakon.

Abdoulaye Yéro Baldé da Faya Millimouno, sun zo na biyu da kashi 6.59% da kuma na uku da kashi 2.04% na kuri’un bi da bi.

Yawan waɗanda suka fito a hukumance ya kai kashi 80.95%, wanda ya ɗan yi ƙasa da yadda aka sanar da farko da kashi 85%.

Yanzu ya rage ga Kotun Koli ta tabbatar da sakamakon zaben.

A cikin sanarwarsu ta karshe, kungiyar sa ido ta Tarayyar Afirka da ta ECOWAS sun lura da rashin manyan jam’iyyun adawa, yayin da suka yaba wa hukumomin Guinea saboda yadda aka gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted