Falasdinawa fiye da dozen biyu ne suka rasa rayukansu saboda tsananin sanyi a Gaza, bayan ruwan sama da iska da aka fara yi a yankin a cikin yan makonni da suka gabata. Banda haka tare da ci gaba da hana kayakin agaji shiga yankin wanda HKI take yi, tun bayan yarjeniyar tsagaita wuta na watan Octoban da ya gabata.
Labarin ya kara da cewa iska da kuma ruwan sama mai yawa da ke sauya a yankin Gaza a cikin yan kwanakin da suka gabata ya sanya rayukan falasdinawa kimani 900,000 da suke rayuwa a bakin ruwan Tekun Medeteranian cikin hatsari saboda tsananin sanyi da kuma ruwan saman da ya cika hemominsu da kuma iska mai karfin da ke tumbuke tentuna ko hemominsu. Kamfanin dillancin labaran WAFA ta falasdinawa ta nakalto kungiyar bada agaji ta Falasdinawa tana bada labarin mutuwar mutane 25 a makon daya gabata. Daga ciki har da kananan yara 3. Labarin ya kara da cewa cutar sanyi da tsananin murace ta kashesu, a dai dai lokacinda HKI take ci gaba da hana shigowar kayakin agaji cikin Gaza. Wanda ya hada da magungu da kuma tentuna masu kwari wanda zasu kare falasdinawa daga tsananin sanyin da ake fama da su a yankin.
Har’ila yau gine –gine da suka lalace kimani 110 suka fada kasa bayan ruwa mai tsanani a cikin yan makonnin da suka gabata a gaza, wanda hakan hatsari ne ga rayukan falasdinawa da dama.