Iran Tayi Gargadin Mayar Da Martani Mai Tsanani Kan Duk Wani Wuce Gona Da Iri A Kanta

Babban mai bawa  jagoran juyin musulunci shawara Ayatullah sayid Imam Khamnai yayi tofin Allah tsine da barazanar da Amurka ta yi a baya bayan nan

Babban mai bawa  jagoran juyin musulunci shawara Ayatullah sayid Imam Khamnai yayi tofin Allah tsine da barazanar da Amurka ta yi a baya bayan nan na kai harin soji kan kasar iran yace mummunan martani na nan tafe ga duk wanda ya kuskura yayi gigin kawo mana Hari

Admiral Ali shamkhani ya bayyana hakan ne a shafuka sada zumunta a jiya litinin inda yayi gargadin cewa duk wani harin da za’a kai wa kasar iran to zai fuskanci mayar da martani nan take, fiye da tununi wanda ya kai harin,

Wadannan kalaman suna zuwa ne bayan da shugaban Amurka Donald Trump yace zai goyi bayan  isra’Ila  ta kai wa iran hari idan iran ta ci gaba da kera makamai masu linzami na ballistic da kuma shirinta na nukiliya,  kuma ya fadin hakan ne ga yan jaridu kafin ganawarsa da prime ministan Isra’ila Binyamin Natanyaho.

Dakarun kare juyin musulunci na Iran sun gargadi makiya game da duk wani rashin lissafi, sun kuma jaddada cewa zasu kare hurumin kasar, tsaro da martabarta da kuma mayar da martani kan duk wani wuce gona da iri, ko harin soji,

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted