MDD ta nemi Birtaniya ta kare hakkokin masu goyon bayan Falasdinawa

Kwararrun Majalisar Dinkin Duniya sun yi kira ga gwamnatin Birtaniya da ta kare hakkin fursunonin da ke goyon bayan Falasdinawa wadanda suka shiga yajin cin

Kwararrun Majalisar Dinkin Duniya sun yi kira ga gwamnatin Birtaniya da ta kare hakkin fursunonin da ke goyon bayan Falasdinawa wadanda suka shiga yajin cin abinci tun daga ranar 2 ga Nuwamba. 

“kwararun sun bayyana ‘babban damuwa’ game da halin da wadannan masu fafutukar kare Falasdinawa takwas da aka tsare da a Burtaniya, wadanda suka shafe kusan watanni biyu suna yajin cin abinci marar iyaka,” in ji Ofishin Babban Kwamishinan Kare Hakkin Bil Adama na Majalisar Dinkin Duniya a cikin wata sanarwa.

“Wajibi ne gwamnati ta kare masu yajin cin abincin, ba ya raguwa,” in ji kwararrun.

Kwararun sun kuma bayyana damuwarsu game da yadda ake kula da masu yajin cin abinci dake tsare.

Sanarwar ta kuma tunatar da cewa kwararrun Majalisar Dinkin Duniya sun riga sun gargadi gwamnatin Burtaniya game da amfani da yaki da ta’addanci wajen hana ‘yancin yin taro, haduwa, da bayyana ra’ayi, da kuma danne ‘yancin fafutukar kare Falasdinu.

Sanarwar ta kara da cewa, “Kwararrun sun kuma nuna matukar damuwarsu game da yadda ake fassara ta’addanci a cikin dokokin Birtaniya, haramta kungiyar Palestine Action a karkashin Dokar Yaki da Ta’addanci ta 2000, da kuma kama mutane da gurfanar da su a gaban kotu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted