Benin: Ana Ci Gaba Da Farautar Wadanda Su Ka Jagoranci Juyin  Mulkin Da Bai Yi Nasara Ba

Majiyar hukumar shari’a ta kasar Benin ta ce, ya zuwa yanzu an kama mutane 30, mafi yawancinsu sojoji kuma ana tsare da su a kurkuku

Majiyar hukumar shari’a ta kasar Benin ta ce, ya zuwa yanzu an kama mutane 30, mafi yawancinsu sojoji kuma ana tsare da su a kurkuku daga jiya 16 Disamba, bayan da aka  gabatar da su a gaban kotun kasar mai shari’ar ta’addanci da kuma yi wa tattalin arziki ta’annati a jiya Talata 16 ga watan Disamba.

Tuhumar da ake yi wa mutanen ta kunshi ‘ Cin Amanar Kasa”, “Kisan Gilla” da kuma ” Jefa tsaron kasa cikin hatsari.”

A yayin da ake zaman shari’ar mutanen an zagaye kotun a tsattsauran tsaro.

A farkon wannan watan na Disamba ne dai wasu sojojin kasar ta Benin su ka yi yunkurin juyin Mulki, sai dai ba a je ko’ina ba,aka sanar da dakile shi.

Kasashen Faransa da Najeriya ne su ka taka rawa wajen dakile yunkurin juyin mulkin, bayan da wadanda su ka shirya shi, su ka sami damar kafe gidan talabijin da fitar da bayani.

Majiyar gwamantin kasar ta ce,da akwai mutanen da su ka rasa rayukansu sanadiyyar yunkurin juyin Mulki, kuma har yanzu da akwai wadanda ake nema ruwa a jallo daga cikin sojojin da su ka jagoranci juyin da su ka hada da laftanar kanar Pascal Tigri.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted