ECOWAS ta bukaci waware batutuwa na siyasa ta hanyoyin lumana a yammacin Afirka

Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ECOWAS ta nuna damuwa kan rudanin siyasa a yankin, kamar yadda kafafen yada labaran Najeriya suka ruwaito. Shugaban

Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ECOWAS ta nuna damuwa kan rudanin siyasa a yankin, kamar yadda kafafen yada labaran Najeriya suka ruwaito.

Shugaban Hukumar ECOWAS Omar Touray ya shaida wa taron ministoci a Abuja babban birnin Najeriya cewa, “Abubuwan da suka faru a ‘yan makonnin da suka gabata sun nuna bukatar yin tunani sosai kan makomar dimokuradiyyar yankin da kuma bukatar saka hannun jari cikin gaggawa a harkokin kasuwanci da tsaro.”

Sanarwar ta zo ne bayan wani yunkurin juyin mulki a kasar Benin a karshen makon da ya gabata, wanda ya biyo bayan nasarar juyin mulkin da aka yi a Guinea-Bissau.

Touray ya ce akwai manyan hadura da dama da suka hada da rashin bin ka’idojin mika mulki a Guinea, da gurgujewar Shirin  zabe, da kuma kalubale ga diflomasiyya da hadin kan kasashe mambobin kungiyar ECOWAS.

Toray ya kuma yi kira da a kara yawan tarurruka tare da yin kira ga kungiyar da ta hada  kai don tunkarar barazanar ta’addanci wadanda ke a matsayin babban kalubale ga duniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted