Borkina Faso Ta Saki Sojojin Sama Na Najeriya 11 Da ta Kama Bayan Jirginsu Yayi Saukar Gaggawa.

Rahotanni sun bayyana cewa gwamnatin barkina faso ta sanar da sakin jami’an sojin saman nigeriya guda 11 da suka yi saukar gaggawa da jirginsu mai

Rahotanni sun bayyana cewa gwamnatin barkina faso ta sanar da sakin jami’an sojin saman nigeriya guda 11 da suka yi saukar gaggawa da jirginsu mai lamba C-130 a birnin Ouagadugu da ta bayyana saukar ta su ta gaggawa ce ba shiri, saboda matsala da jirgin ya samu a cewarsu,

Daga cikin Jami’an soji akwai matuka jirgi biyu sai fasinjoji guda 9 an kamasu domin gudanar da bincike saboda zargin da ake musu na cewa jirgin yana da alaka da juyin mulki da bai yi nasara ba a kasar benin, kafin daga baya a sake su kuma tuni suka isa Najeriya.

A wani bayanin hadin guiwa da gwamnatocin soji na kasashen borkina faso da mali da Niger suka fitar karkashin lemar kungiyar Allience of sahel state sun bayyana abinda ya faru a matsayin keta hurumin sararin samaniyar kasar kuma ya sabama doka, sai dai sun ce lamarin ya sanya jamai’an sojin samansu cikin shirin ko ta kwana.

Najeriya ta ce jirgin ya yi saukar gaggawa ne saboda matsalar da ya samu, sai dai jami’an borkina faso sun yi zargin cewa jirgin ya shiga sararin samaniyarsu ba tare da izinin ba, kuma jami’ansu suna aiki da dokokin tashi da saukar jiragen sama don tsaron kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted