Najeriya : Matsala ce ta sa jirgin sojinmu yin saukar gaggawa A Burkina Faso

Kakakin rundunar sama ta tarayyar Najeriya, wato ‘Nagerian Air Force’ Ehiment Ejodame ya bayyana cewa jirgin wani jirgin saman rundunar dauke da mutane 11 ya

Kakakin rundunar sama ta tarayyar Najeriya, wato ‘Nagerian Air Force’ Ehiment Ejodame ya bayyana cewa jirgin wani jirgin saman rundunar dauke da mutane 11 ya yi saukan gaggawa a kasar Burkina Faso a ranar litinin da ya gabata.

Jiridar Daily Trust ta Najeriya ta nakalto Ejodame yana fadar haka a yau Talata ya kuma kara da cewa kungiyar kasashen AES sun tilastawa jirgin sauka a Bobo Dioulasso na Burkina Faso bayan zargin cewa jirgin ya keta hurumin sararin samaniyar kasar ba tare da izini ba.

A halin yanzu dai ana saran za’a warware matsalar da ke tsakanin kasashen biyu sannan jirgin zai kama hanyarsa zuwa kasar Portigal kamar yadda aka tsara.

Labarin ya kara da cewa, jirgin ya tashi daga birnin Lagos sannan ya fuskanci matsala sannan ta yi saukan gaggawa Bobo-Dioulasso a Burkina faso.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted