Gwamantin Nigeria ta aike da jiragen yaki zuwa kasar Benin domin taimaka wa gwamnatin farar hula domin dakile yunkurin juyin mulkin da aka yi a kasar.
Aikin da jiragen yakin su ka fara yi, shi ne shimfida ikonsu a sararin samaniyar kasar Benin a ranar Lahadin da ta gabata,adaidai lokacin da sojoji da suke biyayya ga shugaba Patrice Talon su ka fafata da sojojin da suka yi kokarin kifar da gwamnati.
Ofishin shugaban kasar ta Nigeria, Ahmad Tininu ya kuma yi bayanin cewa; Daga cikin ayyukan da sojojin na Najeriya su ka yi a tare da hadin gwiwar takwarorinsu na Benin masu biyayya ga gwamnati, shi ne sanya idanu da kuma zama cikin ko ta-kwana domin aikewa da sojoji a kasa.
Ana kuma sa ran cewa sojojin kasashen Saliyo, Cote De Voire da Ghana za su isa Benin domin tabbatar da kare gwamnatin farar hula a karkashin kungiyar tattalin arziki ta yammacin Afirka ( Ecowas).
A mataki na karshe da sojojin Najeriya su ka tsoma baki a wata kasa ta yammacin Afirka shi ne 2017, yayin da shugaban kasar Gambia Yahya Jami’u, ya ki amincewa ya sauka daga karagar mulki duk da cewa bai ci zabe ba.
A duk lokacin da aka yi juyin mulki a cikin kasashen nahiyar Afirka,musamman a yammacinta, kasar Nigeria tana zama ta gaba wajen yin tir da shi. Juyin mulkin da ya gabata na kasar Guinea Bissau, ya sa gwamnatin Bola Ahmad Tinibu ta yi tir da shi, tare da yin kira da a mayar da kasar kan turbar demokradiyya.