Rwanda Da Amurka Sun Rattaba Hannu Kan Tallafin Dalar Amurka Miliyon $228 Na Kiwon Lafiya

Gwamnatin kasar Rwanda ta rattaba hannu a kan yarjeniya na dalar Amurka miliyon $228 a karkashin sabon tsarin taimako na gwamnatin kasar Amurka. Shafin yanar

Gwamnatin kasar Rwanda ta rattaba hannu a kan yarjeniya na dalar Amurka miliyon $228 a karkashin sabon tsarin taimako na gwamnatin kasar Amurka.

Shafin yanar gizo na labarai Africa News ya bayyana cewa tallafin zai taimakawa kasar Rwanda ta kyautata harkokin kiwon lafiya a kasar ta Rwanda a yayinda tallafin kudaden zai ci gaba a sabon tsarin da gwamnatin Amurka ta fitar don tallafawa kasashen kawayenta.

Tun ran Jumma’a ne aka bada labarin kulla wannan yarjeniyar, bayanda shugaba Paul Kagame na kasar Rwanda ya rattaba hannu kan wata yarjeniya ta zaman lafiya tsakaninsa da shugaban kasar Kongo Felix tsetsekedi don kawo karshen yaki a gabacin kasar Kongo wanda kasar ta Amurka ta jagoranta.

Karkashin wannan yarjeniyar dai Amurka zata kashe dalar Amurka miliyon $158 kan kyautata kiwon lafiya a kasar Rwanda ta hanyar yakar cututtuka masu yaduwa wadanda suka hada da HIV da Malaria. Da kuma kyautata tsarin shirin ko ta kwana na bullar cututtuka masu hatsari.

Sannan Kigali zata kara dalar Amurka miliyon $70 a cikin harkokin kiwon lafiya a kasar don bayyana kekyawar anniyarta a cikin shirin kyautata kiwon lafiya a kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted