Sheikh Kassim Ya Yi Suka Akan Shigar Lebanon Cikin Kwamitin Tattaunawa Da “Isra’ila” Kai Tsaye

Babban magatakardar kungiyar Hizbullah Sheikh Na’im Kassim wanda ya gabatar da jawabi a jiya Juma’a da marece ya yi suka akan yadda aka shigar da

Babban magatakardar kungiyar Hizbullah Sheikh Na’im Kassim wanda ya gabatar da jawabi a jiya Juma’a da marece ya yi suka akan yadda aka shigar da farar hula dan kasar Lebanon a cikin kwamitin dake sa ido akan tsagaita wutar yaki da Haramtacciyar kasar Isra’ila, yana mai bayyana hakan da cewa; ya sabawa dukkanin bayanan da su ka rika fitowa a hukumance na ganin an daina kawo wa Lebanon hari sannan ayi hakan.

Jawabin na Sheikh Na’im ya yi shi ne adaidai lokacin da ake tunawa da kuma girmama malaman addini da su ka yi shahada, yana mai cewa abinda aka yi na tura wakilin Lebanon farar hula a cikin wannan kwamitin tsagaita wutar, tamkar bai wa Isra’ila kyauta ne da kuma ja da baya, kuma duk da hakan ba zai sauya matsayar abokan gaba ba, ya daina kai hare-hare ko ya janye daga inda ya mamaye.

Sheikh Na’im Kassim ya kuma ce; Wakilin Lebanon farar hula ya shiga cikin kwamitin amma babu abinda ya karu sai matsin lamba daga “Isra’ila” tare da Amurka da ci gaba da kai wa Lebanon hare-hare.

Babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah ya kuma ce; Wannan abinda ya faru wani Karin koma baya ne, kuma mai makon a dauki matakan da za su bai wa Lebanon karfi, sai ake daukar matakan da ba su ne su ka dace da Isra’ila ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted