Fadar gwamnatin kasar Iraki ta sanar da cewa ba ta masaniya akan yadda aka shigar da sunayen Ansarullah na Yemen da kuma Hizbullah ta kasar Lebanon a cikin jerin sunayen kungiyoyin ‘Yan ta’adda da aka rike kudadensu dake bankunan kasar.
Bayanin fadar gwamnatin kasar ta Iraki ya kuma kara da cewa; Matakai irin wadannan da ake dauka a kasar ba a aike wa da su zuwa fadar gwamantin kasa,abinda ake aikewa fadar shi ne dokokin da majalisar dokokin kasar ta yi, domin a sake tantancewa da kuma amincewa.”
Haka nan kuma sanarwar ta ce; wasu daga cikin abubuwan da ake aikewa fadar mulkin kasar sun hada da tsare-tsaren fadar shugaban kasa,amma abinda ya shafi matakan majalisar ministoci, da na kwamitin dake dakatar da kudaden ‘yan ta’adda da na kwamitin da yake sa ido akan masu wanke kudaden haram, ba a aikewa fadar gwamatin kasar.”
A karshe bayanin ya ce, fadar gwamantin kasar ba ta da wata masaniya akan matakan da aka dauka na bayyana Ansrullah da Hizbullah a matsayin kungiyoyin ‘yan ta’adda tare da daukar matakan hana amfani da kudadensu a cikin bankunan kasar ta Iraki.
Sanarawar da aka yi a kasqar Iraki a shekaran jiya Alhamis na cewa an hana wasu kungiyoyi da su ka hada “Isis, alka’ida, Ansarullah da kuma Hizbullah, amfani da bankunan kasar domin hada-hadar kudade, ya tayar da kura a cikin da wajen kasar. Mutane sun fito kan titutan kasar ta Iraki domin yin tir da wannan sanarwa.
Sai dai daga baya gwamantin kasar ta janye wannan sanarwa.