Limamin Juma’ar Tehran Ayatullah Sayyid Ahmad Khatami ya yi Ishara da yadda tsarin tsaron ‘yan sahayoniya ya rushe a yayin yakin kwanaki 12, yana mai kara da cewa; A wancan yakin na kwanaki 12 an murkushe abokan gaba, don haka idan har su ka sake yin wani gigin to za a sake murkushe su.”
Ayatullah Sayyid Ahmad Khatami ya kuma yi Ishara da jawabin jagoran juyin musulunci na bayan nan da a ciki ya bayyana cewa; Trump da Netanyahu suna cikin wahamin cewa Iran ce aka yi galaba a kanta,amma akasin haka ne ya faru, al’ummar Iran ce ta yi nasara akan Amurka da ‘yan sahayoniya a cikin yakin kwankai 12.
Haka nan kuma limamin na Tehran ya kore cewa; Iran ta aike wa da Amurka wasika, ta hanyar wata kasa, yana mai cewa; Ya kamata su kwana da sanin cewa ba ma aika sako ga Amurkawa wadanda suke cin amanar abokansu ma, kuma ba ma yin tattaunawa da su.
Ayatullah Sayyid Ahmad Khatami ya kuma ce; Ba za mu taba tattaunawa da Amurka ba har sai ta sauya halayyarta, domin abinda Trump yake son fada wa duniya shi ne ya tilasawa Iran zama kan teburin tattaunawa,amma abinda muke fada masa shi ne cewa; wadanda ma su ka gabace ka, daga kan Jimmy Carter har zuwa wadanda su ka biyo bayansu, sun mutu da wannan bakin cikin, kai ma tabbas da wannan bakin cikin za ka shiga kabari.
Ayatullah Sayyid Ahmad Khatami ya kuma ce; Tun tuni taken da wannan juyin yake bayarsa shi ne cewa; Za ,mu yi yaki, mu kuma mutu,amma ba za mu mika kai ga kaskanci ba.”