Najeriya: Tinubu Ya Nada Wasu Karin Jakadu 65, Sanatoci Da Tsoffin Gwamnoni Na Daga Cikinsu

Shugaba Bola Ahmad tinubu na tarayyar Najeriya ya nada wasu karin jakadu 65 wadanda suka hada da sanatoci masu ci da kuma tsoffin gwamnoni har’ila

Shugaba Bola Ahmad tinubu na tarayyar Najeriya ya nada wasu karin jakadu 65 wadanda suka hada da sanatoci masu ci da kuma tsoffin gwamnoni har’ila yau da kwararrun jakadu.

Jaridar Premium times ta Najeriya ta bayyana cewa shugaban ya aikawa majalisar dokokin kasar wasika dangane da hakan, wasika wacce shugaba majalisar dattawa Godswill Akpabio ya karanta a gaban sanatoci a jiya Alhamis.

Kafin haka shugaban ya gabatar da sunayen wasu yan siyasa 3 don nadasu jakadu. A cikin wasikar shugaban yace mutane 34 daga cikinsu kwararrun jakadune, sannan sauran 31 yan siyasa ne.

Daga cikin wadanda shugaba yanada har da tsohon shugaban hukumar zabena kasar (INEC) Farfesa Mahmood Yakubu) sauran sun hada tsoffin gwamnonin jihohin. Enugu, Abia, tsohon mataimakin gwamnan  Lagos, sai sanata Jimo Ibrahim daga jihar  Ondo ta arewa, matar marigayi tsohon gwamnan Oyo  Abiola Ajimobi da matar tsohongwamnan Ekiti Angela Adebayo.

Bayan karanta wasikar shugaban majalisar dattawa ya maida al-amarinsu ga kwamitin harkokin wajen na majalisar don su kammala ayyukansu cikin mako guda kafin a sauraresu a majalisar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted