Microsoft Za Ta Fuskanci Hukunci Kan Taimaka Wa Laifukan Isra’ila A Kan Falasdinawa

Microsoft na fuskantar matsin lamba da kuma matakin shari’a saboda samar wa Isra’ila fasahar da ake amfani da ita wajen take hakkin Falasdinawa a Gaza

Microsoft na fuskantar matsin lamba da kuma matakin shari’a saboda samar wa Isra’ila fasahar da ake amfani da ita wajen take hakkin Falasdinawa a Gaza da Yammacin Kogin Jordan.

A cikin wata budaddiyar wasika da aka aike wa kamfanin a ranar 2 ga wannan watan, wata kungiyar lauyoyi ta kasa da kasa ta yi gargadin cewa Microsoft da shugabanninta za su iya fuskantar hukunci na shari’a kan taimakawa da kuma tallafawa laifukan da aka aikata wa fararen hula Falasdinawa.

Eric Saib, mai kula da harkokin ci gaban kafofin watsa labarun kasa da kasa na Cibiyar Larabawa don Ci gaban Kafafen Yada Labarai, ya  jaddada cewa watannin baya-bayan nan sun nuna karara cewa ana amfani da ayyukan kamfanin wajen take hakkin dan adam a Falasdinu, yana mai kira ga masu hannun jari da su fahimci hadarin da ke tattare da ci gaba da wannan hadin gwiwa.

Wasikar ta bayyana cewa Microsoft tana bai wa sojojin Isra’ila na kasa, sama, da na ruwa bayanai masu mahimmanci duk da amincewa tsakanin kungiyoyin kare hakkin dan adam da kwararru cewa Isra’ila tana aikata kisan kare dangi a Gaza.

A cikin wani rahoto da aka fitar a ranar 30 ga Yuni, Jami’ar Majalisar Dinkin Duniya ta Musamman kan Kare Hakkin Dan Adam, Francesca Albanese, ta nuna cewa kamfanoni sama da sittin daga sassa daban-daban sun ba da gudummawa wajen rusa  Gaza, tallafawa ayyukan gina matsugunan Yahudawa a Yammacin Kogin Jordan, da kuma tilasta wa Falasdinawa yin hijira, ciki har da manyan kamfanonin Amurka kamar Amazon, Google, IBM, da Microsoft.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted